ALUMMR KASUWAR KWARI SUN BUKACI GWAMNA DA TA KAWO MUSU DAUKI.

Wasu daga cikin mazauna kasuwar kwari sun bukaci gwamnatin jiha,karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje  da ta kawo musu dauki,bisa wani ginin toshe hanya da wani attajiri yakeyi a cikin layin gidan labaran dake cikin kasuwar kwari.

Yan kasuwar”sun bayyana cewa watanni uku da suka gabata ne mutumin ya toshe hanya daya,inda ya gina gidan wanka (ba haya) sannan daga bisani cikin kasa da mako biyu ya sake taso da wani ginin hanya.”

Tunda fari dai gwamnatin jiha ta samar da wadannan hanyoyi ne saboda masu wucewa a kafa,lamarin da yasa” Suka ce sanadiyar toshe hanyar suna shan wahala sosai musammam ma masu daukar Kaya.”

Wakilin radion dala Abubakar sabo ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar tsara burane, Wanda yace zasu bincika.

en_USEnglish
en_USEnglish