DALIBAI SAMA DA DARI UKU SUN FAFATA A GASAR MUSABAQA AL`KUR`ANI.

Shugaban kungiyar iyayen yara na makarantar Khalid Bin Walid Islamiyya dake unguwar Ja’en, Mamunu Ibrahim Takai, ya yi kira ga iyayen yara dasu mayar da hankali wajan saka ‘ya’yan su a makarantun islamiyya domin samun ilimin Arabiyya.

Mamunu Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin musabaqar karatun al’kurani mai girma na makarantar da ya gudana a karshen makon da ya gabata.Ya ce” iyaye kada su manta nauyi ne da ya rataya a wuyan  wajan tarbiyantar da ‘ya yansu.”

Shugaban makarantar islamiyyar Khalid Bin Walid Islamiyya, Nasiru Usaini Agalawa, ya ce” ilimi na da matukar amfani ga kowace al’umma,don haka ya zama wajibi iyaye dasu kasance wajan saka ‘ya’yansu a makarantun islamiyya.”

Wasu daga cikin daliban dasu ka yi musabaqar sun nuna godiyar su bisa kammala musabaqar da suka yi.

Wakilin mu Safiyanu Haruna Kutama ya rawaito cewa, dalibai sama da dari uku ne suka fafata a gasar musabaqar.

en_USEnglish
en_USEnglish