YAN`SANDAN SA KAI NA JIHAR KANO,SUN KAI ZIYARA GIDAN MARAYU.

Babban kwamandan ‘yansandan sa kai na jihar Kano, Alhaji Muhammad Bello Dalha, “yace rundunar ta su za ta cigaba da bada gudunmawa don tallafawa yaran da suka rasa iyayen su a rikicin Boko Haram da  ya rutsa dasu.”
Alhaji Muhammad Bello ya furta hakan ne yayin ziyara da rundunar ta kai gidan marayu na Mariri a jiya Lahadi.
Ya ce” ziyarar ta su za ta zama mai daurewa domin tallafawa marayun da kayayakin more rayuwa.”
Shi kuwa Alhaji Mukhtar Gashash kira yayi ga al’umma jihar nan dasu rinka tinawa da marayun domin tallafa masu.
A nasa jawabin shugaban makaranatar marayun Malam Yahaya Salisu Nasarawa, ya yaba da irin wannan ziyarar da ‘yansandan da  suka yi wanda” yace yin hakan zai karfafawa marayun karfin gwiwa.”
A cikin irin kayayakin da suka kai gidan marayun sun hadar da kayan,wasa da na ci da kuma kayan sawa.

en_USEnglish
en_USEnglish