GWAMNATIN JIHAR KANO TA GAMSU DA TSAYAWAR SHUGABAN KASA ZABE A SHEKARAR 2019.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana gamsuwar ta dangane da sake tsayawar takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi a zaben shekarar 2019.

Sanarwar  ta fito ne a cikin wata takarda mai kunshe da sa hannun kwamishinan yada labarai da matasa da kuma al’adu, Kwamrade Muhammadu Garba ya sanyawa hannu.

Ya ce” sake tsayawar takarar ta Shugaban kasa zai yi, na daya daga cikin irin nasarorin da aka samu a cikin shekaru uku ya na kan karagar mulki a kasar nan,musamman ma a bangaren cigaban tattalin arzikin kasar nan wajan farfado dashi daga cikin mashashara da ya shiga,da samar da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa.”

Ya kara da cewar” karkashin jagorancin gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma al’ummar jihar Kano, za su sake marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, wajan ganin ya sake dorawa a kan ayukan da yake yi.”

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish