ISAH SULAIMAN YA SAMI GURBIN ZAMA A GIDAN YARI, BISA ZARGINSA DA AKEYI DA LAIFIN KISAN KAI.

Can kuwa daga kotun majistret mai lamba 15 karkashin jagoranci Alh muntari Garba Dandago, kotun ta aike da wani matashi gidan kaso mai suna Isah  Sulaiman bubbugaje .

Ana dai  zargin matashin da lefin kisan kai, karkashin sashi na 221 na kundin hukunta masu lefi na penal code.

Tun da fari wani mutum mai suna Aminu Bubbugaje ne ya shigar da karar bisa yanda yayi zargin cewar Isa Sulaiman ya kashe masa dansa mai suna Shukurana Lawan, ta hanyar buga masa wuka a kirji sai dai Isan ya musanta zargin .

Tuni dai kotun ta danka shi a hannun jami’in gidan yari,Zakari ya`u har sai ranar 8 ga watan gobe domin cigaba da shari`a.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish