SHUGABAN KASA YA ISA BIRNIN LONDON

A yammacin jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a birnin London na kasar Ingila.

Shugaban  ya tashi daga filin  jirgin sauka da tashi na  Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 4 na yamma sannan kuma ya isa kasar Ingila da karfe 10 na daren jiya.

A na sa ran dai Muhammadu Buhari zai gana da Firime Ministar kasar Therasa May da kuma wasu ‘yan kasar nan mazauna kasar Ingila.

Shugaban kasa zai kuma halarci taron rainon kasashen ingila  a ranar 18 ga watannan wanda zai gabatar da jawabinsa yayin taron.

Haka zalika Muhammadu Buhari, zai kuma gana da shugaban kamfanin main a Royal Dutch PLC,da na kamfanin Shell domin zuba jarin biliyan 15 a fannin man kasar nan.

 

en_USEnglish
en_USEnglish