WATA BABBAR KOTU ANAN JIHAR KANO TA AIKE DA SHUGABAN BANKIN MICRO FINANCE.

Babbar kotun jaha mai lamba 5 karkashin jagorancin mai shari’a Dije Abdu Aboki ta daure wani mutum mai suna Alhaji Munir Muhammad Sagagi shugaban bankin micro finance.

Kotun ta dai daure Mannir sagagi shekara 7 babu zabin tara an kumayi umarnin ya biya ramako na naira miliyan biyar da rabi ga wani mutum mai suna Nasir Abubakar Adam.

Tun da farko dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, itace ta gurfanar da Manniru Sagagi bisa tuhumar hada baki da cuta,wanda kunshin tuhumar ya bayyana irin yanda Mannirun yayiwa Nasiru Abubakar dadin baki ya karbe masa miliyoyin kudi da zummar zai samar masa rancen kudi daga babban bankin kasa CBN.

Wakilin mu na kotu da ‘yansanda, Yususf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa,mai shari’a Dije Aboki ta umarci Mannirun ya biya Nasiru kudinsa ta kuma umarce shi ya zama mutumin kirki idan ya kammala wa adin shekaru 7 kamar .

en_USEnglish
en_USEnglish