GWAMNAN JIHAR KATSINA YA YI KIRA GA AKANTOCIN KASAR NAN

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bukaci Akantoci  a kasar nan da su rinka tonan silili ga manyan jami’an gwamnati da su ke sama da fadi da dukiyar gwamnati.

Aminu Masari ya yi wannan kirar ne yayin da shugaban kungiyar Akantoci  na kasa Alhaji Shehu Ladan ya ziyarce shi a ofishinsa a ranar Talata.

Gwamnan ya ce duk wani babba da ke cikin harkar gwamnati baya iya sanya hanu a kan dukiyar jama’a ba tare da sanin Akanta ba, don haka ne ya ce Akantoci suna da gagarumar rawar takawa wajen rage wawure dukiyar jama’a ta barauniyar hanya.

Ya kuma ce gina kasa gami da samar da ci gaba ba ya taba yuwuwa, sai kowa ya bayar da tasa gudunmawa a fannin sa.

en_USEnglish
en_USEnglish