HUKUMAR HISBA TA JIHAR KANO TA SHA ALWASHIN SA KAFAR WANDO DAYA GA MUTANE DA SUKE HADA CASU.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta yi gargadin kidan casu da wasu mutane suke shiryawa, inda ake samun cakuduwar maza da mata a cikin shigar da bai daceba.

Mataimakin kwamandan hukumar Malam Yakubu Mai Gida Kachako ne yayi wannan gargadi yayin zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, yau a shalkwatar Hukumar.

Ya ce” irin wadannan kade-kade na taimakawa wajan lalata tarbiyyar kananan yara da matasa, baya ga yadda kidan ke damun alumma musamman alokutan sallah.”

Ya kuma kara da cewa, “hukumar ta samu rahotanni kan yadda wasu matasa suke aikata badala a cikin baburan adaidaita sawu. ”

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki  ya rawaito cewa, hukumar ta Hisbah ta kuma bukaci al’umma dasu taimaka wajan dakile ayukan masha’a ta hanyar yiwa mutane nasiha tare da kai rahoton abin da ya gagare su.

en_USEnglish
en_USEnglish