MATASA A NAN JIHAR KANO SUN GUDANAR DA ZANGA-ZANGAR LUMANA A HARABAR OFISHIN KEDCO

Kungiyar matasa mazauna unguwar Zoo Road layout, sun gudanar da wata zanga-zangar lumana da safiyar yau a harabar kamfanin rarraba hasken wutar lantarki KEDCO dake kan titin hanyar zuwa gidan Zoo a nan birnin Kano.

Dandazon matasan sun yiwa harabar ofishin KEDCO tsinke ne bisa wariya da kuma rashin basu wutar lantarki akai-akai lamarin day a haifar da koma baya a harkokin sun a kasuwanci.

Sun kuma kara da cewa, akwai arongizan kudin wuta da kamafin ke yi musu duk da cewa basa samun wutar lantarkin yadda ya kamata.

Kan wannan batu ne wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya tuntubi kakakin kamfanin rarraba hasken wutar lantarkin na KEDCO a nan Kano, Muhammad Kandi ta wayar da tarho, wanda ya ce za su bincika al’amarin.

 

en_USEnglish
en_USEnglish