KUJERUN AIKIN HAJJIN BANA SUNYI KWANTAI A JIHAR KANO.

Hukumar jindadin Alhazai ta jihar kano, tayi fatan samun cinikin kujeru masu yawa wanda yawansu yazarta na shekarar data gabata, inda wasu daga cikin kujerun suka gaza sayuwa.

Shugaban hukumar Muhammada Abba-Danbatta ne ya bayyana hakan a ganawarsu da wakilinmu na ‘Yan zazu yau a hukumar.

Muhammad Abba-Danbatta,” ya ce, ya zuwa yanzu maniyata na cigaba da ajiye kudaden kafin alkalami wanda aka kara wa’adin rufe karba daga karshen watan Maris din daya gabata, zuwa karewar watan afirilun da muke ciki.”

Ya kuma kara da cewa “duk da cewa har kawo yanzu ba’a kai ga yanke tsayayyen farashin kujeraba amma dai ana sa ran ba zau wuce na baraba.”

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa jimillar kujeru dubu biyar da dari biyar jihar kano ta samu a bana.

en_USEnglish
en_USEnglish