RUNDUNAR YANSANDAN KASAR NAN NA CIGABA DA KWATO BINDIGOGI DAGA HANNUN WADANDA SUKA MALLAKA BA BISA KAIDA BA.

Rundunar ‘yansandan jihar Filato ta ce “a kalla ta kwace bindigogi 171 da kuma harsashai sama da dubu daya daga hannun al’ummar gari.”

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar,Jeremiah Undie ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a jihar.

Ya ce” rundunar ta sami nasarar kwato bindigogi 171, da harsashai masu jigida 795 da wasu harsashai 131.”

Ya kara da cewa, “sauran jama’ar da ba su gabatar da makamansu ba, da su yi hanzarin yin hakan kafin cikar wa’adin mayar da makaman kafin nan da karshen watan Afrilu.”

 

en_USEnglish
en_USEnglish