WANI KWARARRAN LAUYA ANAN KANO YA BAYYANA CEWA DUK WATA KOTUN DA BATA DA HURUMIN KARA TO BATA DA HURUMIN TSARE MAI LAIFI.

Wani kwararran lauya anan kano Barrister Abdulkareem maude minjibir ya bayyana cewa duk kotun da bata da hurumin sauraran kara, to bata da hurumin tsare mai laifi.

Barrister maude minjibir ya bayyana hakan ne a yau ta cikin shirin sharia a aikace na nan gidan radion dala.

Yace” babban abinda ya kamata shine duk wata kotu  da tasan bata da hurumi a sharia , to ta rinka sallamar masu kara zuwa wata kotun.”

Barrister ya kuma kara da cewa” akwai hanyoyi da dama da  irin wadannan kotunan zasu magance irin wadannan kararraki.”

A zaman na yau dai an tattauna batutuwa da dama da suka shafi harkokin kotu masu muhimmanci.

 

en_USEnglish
en_USEnglish