WANI MATASHI YA RASA RANSA, YAYIN DA YAKE TSAKA DA AIKIN KAFINTA

Wani matashi mai suna John Ibrahim ya rasa ran sa,  ya yin da yake tsaka da aikin kafinta, a wani kamfani dake, Gunduwawa a karamar hukumar Gezawa.

Matashin John Ibrahim, ya rasa ran na sa ne sakamakon jan wutar lantar ki da ake zargin ta yi masa lokacin da yake tsaka da aikin.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da gidan radiyon Dala cewa ya taba wayar wutar ne da magwajin da yake auna katako a cikin rashin sani lamarin da yasa wutar ta fado da shi kasa daga saman benen da yake aiki.

Wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito cewa ya tuntubi daya daga cikin jami’in gudanarwar kamfanin mai suna Adam A Bello wanda ya tabbatar da mutuwar matashin bayan sun kai shi asibiti.

en_USEnglish
en_USEnglish