WATA BABBAR KOTUN JIHAR TA WANKE WANI MUTUM BISA ZARGINSA DA AKEYI DA CIN ZARAFIN KARAMAR YARINYA.

Babbar kotun jiha mai lamba 4 karkashin mai sharia Ahmad Tijjani badamasi, ta wanke wani mutum  mai suna Ibrahim Abubakar dan kimanin shekaru 86 wanda ake zarginsa da lefin cin zarafin karamar yarinya.

Tun da fari dai yansanda ne suka gurfanar da shi a gaban kotun majistrt mai lamba 16,inda suke zargin shi da lefin yiwa karamar yarinya fyade sai dai daga karshe ma aikatar sharia sun zafafa bincike, inda suka gurfanar da shi a gaba mai sharia Badamasi da tuhumar cin zarafin karamar yarinya.

lauyar gwamnati ta gabatar da shaidu 4 shi kuma wanda ake tuhuma yakare kan sa.

Kotun ta wanke shi bisa la`akari da takardar likita wadda ta takardar ta kunshi cewa babu abin da akayiwa yarinyar, jim kadan da wanke shi Ibrahim Abubakar yayi godiya ga Allah bisa yanda yace gaskiya tayi halin ta.

 

en_USEnglish
en_USEnglish