ANYI MUHIMMIN KIRA GA MATASA.

Wani malami a sashen koyon illimin addinin musulunci na jami’ar Yusuf Maitama Sule, Dakta Ibrahim Ilyas, ya ja hankalin al’ummar musulmi da su mayar da hankali wajan gudanar da yin Sallar Asubahi bisa falalar dake tattare da ita.

Dakta Ibrahim Iliyas, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da wakilin mu Umar Usman Gama a ofishin sa.

Ya ce “akwai a zaba mai zafi da A….h (SWT) ya tanadar ga mai wasa da sallar.”

Dakta Ibrahim ya kuma yi kira da daukacin musulmi da su saka addinin su a gaba fiye da komai na rayuwarsu.

 

en_USEnglish
en_USEnglish