KUNDIN TSARIN MULKIN KASAR NAN YA BAIWA KOWA DAMAR TOFA ALBARKACIN BAKINSA.

Wani kwararren lauya anan Kano Barista Umar Usman Danbaito , ya bayyana cewa doka ta bawa dukkan dan kasa  damar fadin albarkacin bakin sa, matukar babu kazafi ko cin mutuncin wani.

Barista Danbaito ya bayyana hakan ne yau ta cikin shirin sharia a aikace na nan gidan radion dala.

Yace “idan akayi la`akari da sashin nan na 39, daya bawa duk wani dan kasa damar fadin albarkacin bakinsa, a don haka kowani dan kasa na da damar yabo ko sukar gwamnati,matukar mai saba ka`ida ba.”

Barrister ya kara da cewa “hana mutum fadar albarkacin bakinsa tamkar yiwa kundin tsarin mulkin kasa karantsaye ne.”

Barrister danbaito ya kuma ja hankalin al`ummar kasar nan cewa duk da damarmakin da kundin tsarin mulkin ya bayar ,bai kamata mutum ya wuce gonad a iri ba.

 

en_USEnglish
en_USEnglish