AL’UMMAR UNGUWAR KURNA SUN KOKA.

Al’ummar unguwar Kurna layin falwaya sun koka dangane da yunkurin gine masu makabartar da suke zargin wani mutum da jagoraran ta.
Tun farko dai alummar yankin rana tsaka suka ga tarin wasu matasa da kayan aiki suna kokarin aza harsashin gini a makabartar lamarin da yasa mutanen yankin suka ce ba za su laminta ba.
Sun kuma bayyyana cewa basa goyon bayan ayi wani abu da  ba alumma ne za su amfana ba.
Malam Yau Yahaya shi ne mai unguwar Kurna C ya bayyana cewa ba wani wanda zai mallake wurin, sai dai za a ginawa alummar yankin, makarantar firamare.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya tuntubar jami’in kula da harkokin kasa a karamar hukumar Dala wanda yace “lamarin yana hannun Dan Majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Dala”.

en_USEnglish
en_USEnglish