BANKIN DUNIYA YA YI HASASHEN BUNKASAR TATTALIN ARZIKIN KASASHEN AFRIKA.

Bankin duniya ya yi hasashen bunkasar tattalin arzikin kasashen Afrika da kashi 3.1 bisa 100 a wannan shekarar ta 2018 sakamakon farfadowar da suke samu bayan da suka fuskanci koma baya cikin shekaru ukun da suka gabata a sanadiyyar faduwar farashin kayayyaki a kasuwannin duniya.

A cikin wani rahoton hasashe da bankin ya fitar game da tattalin arzikin Afrika, wanda ya saba wallafawa sau biyu a shekara ,yayi hasashen za’a samu bunkasar tattalin arzikin na Afrika da kashi 3.6 bisa 100 a shekarar 2019, da kuma kashi 3.7 bisa 100 a shekarar 2020.

Ana sa ran wannan hasashe zai kara janyo hankalin masu zuba jarin kasashen waje a nahiyar, da suka hada da kasashe masu tasowa kamar kasar Sin, da wasu kasashen duniya da suka ci gaba ta fuskar karfin tattalin arziki, lamarin da ake ganin zai kara yawan hada- hadar cinikayya a kasashen Afirka, kamar yadda rahoton ya nuna.

Kasar Sin ta kasance kasa mafi yawan zuba jari a nahiyar Afrika, a hannu guda kuma, ita ce kasar da ta fi samar da kudaden gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a nahiyar ta Afrika.

 

en_USEnglish
en_USEnglish