FITACCEN LABARIN MAKO

Sandar majalisa wata alama ce ta iko wacce idan babu ita ba za’a iya gudanar da zaman majalisa ba.

Anshiga rudani acikin majalisar dattijai ta kasa a safiyar ranar laraba, 18,04,2018,  yayin da wasu yan daba suka kutsa kai cikin majalisar domin dawo da dakataccen dan majalisa OVIE OMO AGEGE,  yan daban sunyi amfani da karfi akan jami’an tsaro sannan suka dauke sandar majalisar da misalin karfe 11:30 na safe.

Maharan wanda yawansu yakai mutum goma sha biyar sunzo ne a motoci guda uku suka ajiyesu a gaban kofar majalisar tarayya, wasu daga cikinsu suka tsaya domin gadin kofar shiga majalisar tarayya, yayin da wasu suka tsaya suna gadin motocinsu, bayan misalin minti biyar da sauka da cikinsu motocinsu, mutane uku daga cikin yan daban suka shiga cikin majalisar suka fito da sandar majalisar suka shiga cikin motocinsu domin su tsere, yayin  da sukazo fita ta kofar majalisar sai suka ga an rufeta, sai suka juya da baya suka fita ta kofar da ta hada majalisar tarayya da gidan shugaban kasa, wacce ake kira da “VILLA GATE” ta wannan kofar suka samu nasarar tserewa a guje.

Bayan lokaci kadan yan majalisar Dattaijai suka bude majalisar bayan sun rasa abin yine daga baya aka gane sun shiga mitin na gaggawa a sirrance.

A wannan rana da al’amarin ya faru mataimakin shugaban majalisar Eke okweremadu shi yake shugabantar majalisar, sakamakon shugaban majalisar Bokolo Saraki yana kasar amurka domin wakiltar taron bankin duniya da bankin tallafi na duniya.

Ovie Omo Agege sanata ne da yake wakiltar Dalta ta tsakiya a majalisar tarayya,kuma shine wanda ake zargi ya jagorancin shigar da yan daba  cikin majalisar,a kokarinsu na dawo dashi majalisar bayan an dakatar dashi.

Gungun jami’an tsaro wanda kwamishinan yan sanda Sadik Abubakar Bello ya shugabanta ne zuwa cikin majalisar suka kama Sanata Ovie Omo Agege ta karfi, saidai sunyi artabu kafin su kamashi sakamakon goyon bayansa da wasu daga cikin yan majalisar sukayi, yan majalisar da suka nuna goyon bayansu ga Ovie Omo Agege sune; Sanata Nelson Effighem wanda yake wakiltar  Akwa ibom, da Taiyo Alasadura wanda yake wakiltar Ape ta Ondo, da kuma Sanata Adrew Uchedu daga jihar Rivers.

A jawabin da mataimakin majalisar yayi acikin kwaryar  majalisar yayi godiya ga sanatocin akan goyon bayan da suka bayar yayin faruwar al’amarin, yace, “A wannan safiyar abu wanda ba’a saba dashi ba ya faru da misalin karfe 11:30 na safe wasu yan daba sun kawo hari cikin  majalisa , suka ci mutuncin wasu daga cikin ma’aikatan majalisa, da kuma wasu daga cikin manema labarai na yan jarida, sukayi amfani da karfi wajen dauke sandar majalisa,suka gudu, kuma sun gwada yunkurin yin garkuwa da biyu daga cikin Sanatocinmu, wannan cin mutunci ne ga Sanatoci da kuma Damakwaradiyya da majalisar tarayya gaba daya, amma zamu kasance tsintsiya daya wajen gabatar da aikin da yan kasa suka dora mana wajen wakiltarsu, zamu yi bincike wajen gano wannan matsalar,na tabbatar da cewa na  fadi abinda yake zuciyar sauran yan majalisa”.

Bayan awa ashirin da hudu da faruwar al’amarin, Jami’an tsaro sun gano Sandar majalisar a hanyar fita daga garin Abuja inda yan daban suka yar dashi sakamakon tsaurara matakan tsaro da akayi acikin garin na Abuja.

Saidai wata kotu da take acikin garin Abuja ta haramtawa Jami’an tsaro kara kama Sanata Ovie Omo Agege har sai an tabbatar da zargin da ake yi masa.

 

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish