GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA YUNKURO.

Kwamishinan Ilimn Kimiyya da Fasaha na Jihar Kaduna, Alhaji Jafaru Sani, ya bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna nan ba da jimawa ba za ta ci gaba da daukar malaman firamare a jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Kaduna.

Jafaru Sani ya ce, ” yanzu haka Hukumar Ilimi ta Bai daya ta kammala duk aikin daukar malaman firamare kashi na farko, wanda bayan jarrabawa da ganawa, da tantancewa, an samu nasarar daukar malamai 11,395 cikin malamai 25,000 da za a dauka.

Yanzu haka wadannan malaman an tura su kananan hukumomi da makarantun da za su koyar”

Sannan game da ci gaba da daukar sauran cikon malaman, kwamishinan ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za su ci gaba da wannan aiki na daukar malaman firamare har sai an samu kwararrun malamai 25,000 da Gwamnatin Jihar ke son ta dauka.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Gwamnatin Jihar Kaduna za ta dauki kwararrun malamai guda 25,000 don haka yanzu bayan an tace, an tankade mun samu nasarar daukar malamai 11,395, kuma duk an tura su inda za su yi aiki. Bayan haka, muna da takardun masu neman aikin koyarwa akalla 19,000 a kasa nan ba da jimawa ba za mu yi masu jarrabawa don cike gurbin 25,000 din da muke son dauka. Sannan za a ci gaba da daukar malaman firamare har sai ya zamana kowane malami yana karantar da daliban da ba su wuce 40 a aji ba,kwamishinan ya kara da bayyana cewa, “Kamar yadda aka sani a wannan daukar malaman, mun karbi takardun neman aiki na sama da mutum 40,000, muka tantance muka rairaye muka fitar da sama da mutum 25,000 da suka zauna jarrabawar. Sannan kuma sama da mutum 15,000 suka sami nasarar cin jarrabawar.  Bayan nan kuma wurin ganawa da kara tantancewa muka sami malamai 11,395 wadda yanzu haka an tura su makarantun da za su koyar”.

Haka kuma game da sabon tsarin albashi, kwamishinan ya ce, “Mun yi kudurin fara biyan albashi da sabon tsarin albashi a watan da ya gabata, amma saboda rashin kammala aikin daukar sababbin malaman nan, shi ya sa muka bari sai an kammala duka,yanzu haka muna sa ran duk ranar da za a fara biyan sababbin malaman firamaren da aka dauka, za a fara da sabon tsarin albashi kamar yadda aka yi alkawari, kuma wannan zai hada har da tsofaffin malamanmu”.

en_USEnglish
en_USEnglish