HUKUMAR LAFIYA TA DUNIYA WHO TACE ZA TA KASHE MAKUDAN KUDADE.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce za ta kashe makudan kudade har dala miliyan 178 a harkokin lafiya dake fadin kasar nan tin daga cikin shekarar nan da muke ciki har zuwa 2019.

Wakilin mai kula da ofishin hukumar a kasar nan,Dakta Wondimagenehu Alemu ne ya bayyana hakan yayin taron wani hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.

Ya ce dala 127 waanda kasha 66 cikin dari na kasafin kudin, za a kasha su ne wajen tsare-tsaren maganin shan inna.

Ya kara da cewa dala miliyan 30 kuma za a kashe su ne wajan maganin zazzabin Maleria da tarin fuka da kuma cutar kanjamau.

 

en_USEnglish
en_USEnglish