AN GUDANAR DA AIKIN IDO GA ‘YAN GUDUN HIJIRA

Kwamatin shugaban kasa kan ‘yan gudun hijira dake Arewa maso gabashin kasar nan, ya ce ya gudanar da aikin ido kyauta ga ‘yan gudun hijira sama da 5000 a yankin.

Shugabar kwamitin Amina Maibe ce ta bayyana hakan yayin ziyarar aikin idanu da ya gudanar a asibitin garin Maiduguri dake jihar Borno.

Amina Maibe ta kara da cewa a kalla an shafe makonni biyu ana gudanar da aikin idanun kyauta ga ‘yan gudun hijirar, wanda hadin gwiwa ne da gwamnatin jihar Borno da kuma wata kungiya.

en_USEnglish
en_USEnglish