AN KWANTAR DA GEOGE H.W BUSH A ASIBITI.

An kwantar da tsohon shugaban Amurka, George H.W. Bush, a wani sashe da ake kula da masu cutar da ta yi tsanani a asibitin garin Texas, ‘yan kwananki bayan rasuwar matarsa,
A wata sanarwa da mai magana a madadin iyalan tsohon shugaban, Jim McGrath ya fitar, yace, “Tun ranar Lahadi aka kwantar da Bush Babba, mai shekara 93, bayan ya kamu da wata cuta da ta yadu a jininsa.
Sai dai mai magana da yawun iyalan na Bush ya ce yana samun sauki.
Shekara daya da ta wuce a daidai wannan watan Mista Bush ya shafe mako biyu a asibiti domin jinyar cutar sanyin hakarkari da kuma ta wata mai tsanani ta huhu.
A yanzu dai George Bush shi ne tsohon shugaban kasar Amurka mafi dadewa da ke a raye, kuma y yi shugabancin ne tsakanin 1989 da 1993.

en_USEnglish
en_USEnglish