KAMATA YAYI A TSIGE SHUGABA BUHARI.

Majalisar wakilan kasar nan ta nuna fushinta game da yanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da makudan kudade, kimanin Dala miliyan dari hudu da casa’in da tara. Kwatankwacin Naira Biliyan dari da hamsin da shida, ba tare da sahalewar majalisar ba, dan siyan jiragen yaki da makamai daga kasar Amurka.
Wasu daga cikin yan majalisar sun nuna rashin jin dadinsu da bayyana cewa ko kadan abinda shugaban yayi bai dace ba kamata yayi a dauki matakin tsigeshi da kan mulki.
A takardar da shugaban ya aikewa majalisar ya bayyana cewa ya dauki matakin ne kai tsaye, ba tare da tsammanin zasu kawo cikas kan abinda yayi ba, tuni kasar Amurka ta bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta biya kudaden Jiragen yakin da makaman da ta siya dan yakar yan tada kafar baya na na Boko haram.

en_USEnglish
en_USEnglish