ANYI KIRA GA YAN JARIDU.

Shugaban kungiyar yan jaridu na jihar Kano, Kwamarade Abbas Ibrahim, ya bukaci ‘yan jaridu a fadin jihar nan da su rinka shiga loko da sako domin kara wayar da kan al’umma dangane da matsalolin zazzabin cizon sauro da ma yadda cutar take kara yaduwa.

Kwamrade Abbas, ya bayyana hakan ne yayin taron wayar da kai ga ‘yan jaridu a jiya Lahadi.

Ya kuma ce ta haka ne ‘yan jaridun za su bada gudunmawar su ga al’umma don magance cutar zazzabin cizon sauro.

A nasa jawabin shugaban kungiyar masu rajin rage cutar zazzabin cizon sauro a nan Kano, Yusuf Muhammad Gwammaja, ya ce sun dauki gabaran hakan ne don magance yaduwar cutar.

Shi kuwa Sarkin tsaftar Kano, Alhaji Jafaru Ahmad Gwarzo, ya ce wayar da kan al’umma ita ce hanya daya da za a dakile yaduwar cutar.

 

en_USEnglish
en_USEnglish