BABU CUTAR POLIO A JIHAR KANO.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bayyana cewa, babu wata sauran cutar Polio guda daya a dukannin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar nan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin kwamishinan lafiya Dakta Kabiru Ibrahim Getso daya wakilce shi, yayin kaddamar da rigakafin allurar Polio zagaye na biyu da aka gudanar a garin Danfadal dake karamar hukumar Wudil.

Ya kuma bukaci iyaye da sauran jami’an lafiya cewa kada su yi wasarairai da harkokin lafiya, musamman ma tabbatar da ganin kowane yaro ya samu allurar yadda aka tsara a garuruwan su, domin kaucewa sake fadawa cikin matsalar cutar da ma sauran cututtuka masu yaduwa irin su sankarau, zazzabin cizon sauro da dai sauran su.

Ya kara da cewa, sama da yara miliyan 2.5 ne ‘yan kasa da shekaru biyar ake sa ran yiwa allurar rigakafin a kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano.

en_USEnglish
en_USEnglish