KIRA GA MASU HANNU DA SHUNI.

Na`ibin limamin masallacin juma’a na Zera dake gandun Albasa a karamar hukumar birni, malam Muhd Auwal Ishaq garangamawa,yayi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni dasu rinka shigowa cikin harkokin tallafawa marayu da gajiyayyu domin samun falala mai tarin yawa a ranar gobe alkiyama.
Malam Muhammad Garangamawa yayi wannan kiran ne, yayin taron tallafawa marayu da gajiyayyu,da ya gudana a dakin taro na gidan Bashir Tofa karo na goma sha shida a karshen makon daya gabata.
Yace rikon maraya na da matukar lada a addinance,domin barin su kara zube, zai iya haifar da babbar illa a unguwanni.

en_USEnglish
en_USEnglish