AN UMARCI HUKUMOMIN DAKE DA RUWA DA TSAKI.

Gwamnatin tarayya ta haramta hadawa da kuma shigar da magungunan tari masu kunshe da Kodin a cikin kasar nan, a wani mataki na kawo karshen yadda ake amfani da maganin ba bisa ka’ida ba, musamman tsakanin matasa.
Ministan lafiya Isaac Adewole ya ce, gwamnati ta umarci hukumomin da abin ya shafa, da su aiwatar da wannan haramci, wanda ya hada da dakatar da ba da iznin shigo da sinadarin na Kodin da ake amfani da shi wajen hada maganin tari.
Ministan ya kuma ce gwamnati ta haramta sayar da duk wani maganin tari mai kunshe da Kodin ba tare da izinin likita ba.
A cewarsa, an kuma umarci hukumomin gwamnati da su sanya ido kan yadda za a rika sanya alama a jikin maganin da yadda ake siyar da maganin tari mai kunshe da Kodin a dukkan fadin kasar nan.
Gwamnati dai ta dauki wannan mataki ne, biyo bayan wasu rahotanni game da yadda ake samun karuwar ta’ammali da wadannan magungunan a kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish