KOWANI DAN KASA NADA DAMAR MALLAKAR MUHALLI.

Kwararran lauyan addinin musulunci Barista Umar Usman Danbaito, ya bayyana cewa, sashi na 43 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa kowane dan kasa damar mallakar muhalli a ko ina a fadin kasar nan.

Barista Danbaito ya bayyana hakan ne a yau bayan kammala shirin “Shari’a a aikace” na gidan rediyon Dala.

Ya ce koda gwamnati za ta karbi muhallin mutum bayan ya mallaka sai an biya shi diyya.

Ya kuma ce duk wanda gwamnati ta karbarwa kadara ba tare da ta bashi shaidar karba ba, yana da damar garzayawa kotu don neman hakkin sa.

Barista Umar Usman Danbaito, ya kuma shawarci al’umma dasu rinka zuwa kotu duk lokacin da aka karbarwa mutum kadara ba bisa ka’ida ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish