MATAIMAKIN SHUGABAN KASA YAYI KIRA GA JAMI’AN TSARO.

Gwamnatin tarayya ta umarci jami’an tsaron kasar nan da su tsaurara matakan tsaro a kasuwanni da sauran wuraren ibada a garin Mubi dake jihar Adamawa.
Mataimakon shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da kakakin sa Laolu Akande ya sanyawa hannu.
Ya ce,|” sakamakon wani harin kunar bakin wake da bama-bamai da aka kai wani masallaci dake kasuwar garin Mubi a jiya, harin yayi sanadiyar kashe akalla mutane 24 tare da jikkata wasu mutane da dama.
Osinbanjo, ya kuma umarci hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da ta gaggauta samar da magunguna da sauran kayayyakin agaji ga wadanda lamarin ya shafa.
Ya kuma tabbata cewa jami’an tsaron kasar nan na kokarin gano tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danyan aikin,sannan kuma ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadan suka mutu.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin.

en_USEnglish
en_USEnglish