ZA A SAMAR DA AIKIN YI GA MATASA A KALLA 100,000

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo, ya kaddamar da wani shirin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin wadanda suka kammala karatu, mai taken “Nation Builders Corps” ko NABCO a takaice.
Cikin shekarar nan kadai, Shirin zai ba da damar samar da aikin yi ga mutasa a kalla 100,000 wadanda ke da shaidar digiri, a ma’aikatun gwamnati domin biyan bukatun kasar.
Nana Akufo Addo ya ce rashin aikin yi tsakanin matasa ya kasance abun takaici ga rayuwar al’ummar kasar, kuma a baya-bayan nan, matsalar ta yi kamari biyo bayan haramcin daukar aiki a bangarorin gwamnati da asusun ba da lamuni na duniya ya yi.
Shugaban kasar na da yakinin cewa, zuwa lokacin da za a kammala daukar horo daga shirin na NABCO da zai shafe tsawon shekaru 3, za a magance matsalar rashin gogewa da fasahohin da ake bukata, wadanda ke wa matasan tarnaki wajen samun aikin yi a matsayinsu na sabbin wadanda suka kammala karatu.

en_USEnglish
en_USEnglish