AN SAMU RUSHEWAR GIDAJE A JIHAR KANO.

Sakamakon mamakon ruwan sama da iska da a aka tafka a yammacin jiya Laraba a wasu sassan unguwanni dake kwaryar birni a nan Kano, ya yi sanadiyar rushe wasu gidaje a yankin unguwar Mai Dile da Rigar kuka a karamar hukumar Kumbotso.
Wasu mazauna yankin sun shaidawa wakilin mu na ‘yan Zazu cewa yanayin ruwan saman a jiya, ya zo musu babu zato babu tsammani.
Sun kara da cewa yanayin ruwan ya ja masu asarar tarin dukiya mai dimbin yawa.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, sama da gidaje goma ne suka rushe wanda,al’ummar yankin suka dauki gabarar gyara muhallin su domin tseratar da rayuwar su.

en_USEnglish
en_USEnglish