RANAR YANCIN YAN JARIDU TA DUNIYA.

Kungiyar dake rajin kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya ta bayyana cewa, yawan ‘yan jaridun da aka kashe cikin watanni hudu na farkon shekarar 2018 a kasashe 18 ya karu zuwa 44, sabanin 28 a shekarar bara.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a birnin Genevan kasar Switzerland Yayin da ake bikin ranar ‘yancin ‘yan jaridu ta duniya a yau Alhamis.

Ta ce, daga watan Janairu zuwa Afrilun wannan shekara, yawan ‘yan jaridun da aka kashe ya karu da kaso 57 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gaba ta.

Haka kuma kungiyar ta kuma ce, ta kadu matuka! game da kisan ‘yan jaridu 9 yayin da wasu bama-bamai biyu da suka tashi a Kabul, babban birnin Afghanistan a ranar 30 ga watan Afrilu, inda ta yi Ala wadai da kakkausar murya kan yadda wani ‘dan kunar bakin wake ya yi badda kama a matsayin mai daukar hoto ya tayar da bam din dake jikinsa a cikin cunkoson jama’a, ya kuma hallaka manema labarai.

Kungiyar ta kara da cewae kasashe mafiya hadari a farkon wannan shekara sun hada da Afghanistan, inda aka kashe ‘yan jarida 11, sai Mexico 4, Syria 4, Ecuador 3, a Indiya da Yemen kuma an kashe ‘yan jaridu uku-uku. Yayin da a kasashen Brazil da zirin Gaza da Guatemala da Pakistan kuma aka kashe ‘yan jaridu bibbiyu.

Sai kuma kasashen Colombia da Haiti, da Iraki da Liberiya da Nicaragua da Rasha da El-Salvador da Slovakia wanda aka kashe ‘yan jaridu daddaya kowanne.

Majalisar dinkin duniya dai itace ta ware kowace ranar uku ga watan Mayun kowacce shekara a matsayin ranar ‘yancin ‘yan jaridu ta duniya.

 

en_USEnglish
en_USEnglish