YA KAMATA IYAYE SU MAYAR DA HANKALI A KAN ILMIN YAYANSU.

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci iyaye dasu mayar da hankali wajan kula da ilimin ‘ya’yan su domin ganin sun sami ingantaccen ilimi don amfanin rayuwar su a nan gaba.
Kwamishinan ayuka na musamman Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan ta bakin wakilinsa Umar Yusuf Kashe Kwabo, a jawabinsa da yayi a wajan karrama wasu mutane da suka bada gudun mawa a cikin al’umma wanda makarantar kira’atul Qur’an Islamiyya dake unguwar Gaida Kashu a karamar hukumar Gwale ta shirya.
Ya ce ta hanyar samun ingantaccen ilimi ne ake zama ingatattun mutane a cikin al’umma.
A nasa jawabin Kansilan Ilimi na karamar hukumar Gwale, Alhaji Aliko Anas, ya bayyana cewa, a shirye karamar hukumar take wajan taimakawa makarantar da kayan aiki, domin ganin an samu ingantaccen ilimi atsakanin al’umma.
Wakilin mu Abubakar Sabo, ya rawaito cewa an bude ajujuwa biyar yayin taron baya ga karrama wasu mutane uku da suke baiwa ilimi gudun mawa a yankin na Gaida Kashu ciki harda, Sakataran Ilimi na karamar hukumar Gwale da kuma shugaban makarantar Ahmad Kawu.

en_USEnglish
en_USEnglish