TAWAGAR A.U TA ISA KASAR SUDAN.

Tawagar tarayyar kungiyar Afrika A.U, ta isa kasar Sudan don nazarin ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya da kuma halin da ‘yan gudun hijira ke ciki a kasar.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi, ta ce, kwamitinta na sulhu ya fara ziyarar yini 5 a ranar Aasabar da ta gabata a yankunan birnin Khartoum da kuma Dafur.

Kwamatin zai yi nazarin ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin tarayyar Afrika da MDD, la’akari da aikin nazarin shirin da ake a yanzu, wanda ke nufin duba yiwar janye shi daga kasar.

Har ila yau, kwamatin zai kuma bukaci bangarorin Sudan su mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Dafur, biyo bayan warware rikicin da ya shafe kusan shekaru 15.

Sanarwar ta ce, ziyarar da kwamatin yakai a dai-dai lokacin da aka samu ingantuwar yanayin tsaro, wanda ke bukatar janye shirin a hanakali.

en_USEnglish
en_USEnglish