MAHARA SUN KASHE SAMA DA MUTANE HAMSIN A BIRNIN GWARI.

Masarautar birnin Gwari ta tabbatar da mutuwar sama da mutane hamsin da aka kai musu hari a garin Gwaska’ na karamar hukumar birnin Gwari dake jihar Kaduna.

Yayin ganawa da manema labarai, Sarkin Gwari Mallam Jirbin Zubairu Mai Gwari na Biyu, ya ce sun yi jana’izar kimanin mutane 34, yayin da wasu kuma suka mutu a wasu kauyukan karamar hukumar birnin Gwari.

Lamarin dai ya faru ne kasa da mako guda bayan da wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Janruwa inda suka kashe wasu masu aikin hakar ma’adanai da dama.

Maharan wadanda ake kyautata zaton sun fito ne daga wasu dazuzzuka na jihar Zamfara sun kone kusan daukacin gidajen dake kauyen Gwaska da kuma kauyen Kuiga.

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa, akasarin wadanda aka kasha ‘yan sakai ne dake kokarin kare garuruwansu daga hare-haren ‘yan bindigan da suka addabi al’ummar yankin.

Sai dai a lokacin da ya ziyarci yankin a kwanannn babban Sufetan ‘yansandan kasar nan Ibrahim K. Idris ya yi alkawarin tura ‘yansanda yankin na birnin Gwari don tabbatar da tsaro a yankin.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi alawadai da wasu mahara suka kai yankin Birnin Gwari a karshen makonnan wanda yayi sanadiyar muaten da dama tare da kona tarin dukiya a yankin.

Gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakinsa Samuel Aruwan, a jiya Lahadi.

Ya kuma yi alawadai da kai harin tare da mika ta’aziya sa ga al’ummar yankin birnin Gwari da kuma masarautar.

Gwamna Elrufa’i ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar wato NEMA, da ta gaggauta samar da kayayyakin agaji ga wadanda harin ya rutsa da su.

Ya kara da cewa, tuni gwamnatin  tarayya, da ta jiha ta umarci kafa bataliyar sojoji na dindindin a yankin birnin Gwari domin samar da cikakken tsaro.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish