AN AYYANA RANAR SHA DAYA GA WATAN MAYU A MATSAYIN RANAR HUTU A JIHAR KANO.

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar  Juma’a sha daya ga watan mayu a matsayin ranar hutu a jihar kano ga daukacin ma’akata, a hukumomi da ma’aikatun gwamnati, kamfanoni da cibiyoyi masu zaman kansu.
Wata sanarwa da kwamishinan labarai Mohammed Garba ya fitar yace, ” gwamnati ta bada hutun ne domin baiwa al’umar musulmi damar halatar jana’izar marigayi Sheikh Isyaka Rabiu wanda ya rasu ranar talatar data gabata.
Sanarwar tayi bayanin cewa, fitar da gobe juma’a a matsayin ranar hutu, wata karramawa ce ga marigayin la’akari da dinbin gudunmawar daya bayar wajen cikin tattalin arziki, da lamuran addinin musulunci a ciki da wajen jihar Kano.
A yau alhamis ne ake sa ran isowar gawar marigayi Halifa Isiya ka Rabiu daga birnin London kuma a gobe Juma’a ne za’a yi masa jana’iza a masallacin Jumma’a dake gidan sa a Goron Dutse kan titin Aminu Kano a nan birnin Kano

en_USEnglish
en_USEnglish