HUKUMAR WASANNI TA KANO NA NEMAN HADIN KAN KANANUN HUKUMOMI.

Shugaban hukumar wasanni na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Galadima, ya yi kira ga shugabannin kananan hukumi 44 a nan jihar, da su bada hadin kai dan ganin an sami nasara a wasannin da hukumar ta shirya gudanarwa a fadin jihar nan.
Ibrahim Galadima ya yi kiran ne ya yin da ya kai ziyara kananan hukumomin Gwarzo da Bichi tare da kaddamar da mutane biyu a kowacce shiyya da za su taimakawa kananan hukumin gudanar da aikin gasar.
Yace gasar wasannin na da matukar mihimmanci a tsakanin matasan da ke kananan hukumomin jihar nan domin zai kara haifar da dankon zumunci a tsakanin al’umma.
A jawabin shugannin kananun hukumomin, shugaban karamar hukumar Gwarzo wanda ya sami wakilcin shugaban sashin wasanni, Alh Kabiru Dan azumi Dawakin tofa dana Bichi wanda ya sami wakilcin daraktan mulki, Alh Hudu Sulaiman sun tabbatar da bada hadin kai da goyon baya yayin fara gasar.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa wasannin  za a gudanar dasu a watan Yuni, a cikin wasannin akwai wasan tseren keke da na gudu da kuma wasan kwallon kafa.

en_USEnglish
en_USEnglish