MAJALISAR ZARTARWA TA AMINCE DA BADA LASISIN KAFA JAMI’AR SKYLINE.

Majalisar zartarwa ta kasa ta bada lasisin wucin gadi domin kafa Jami’a mai zaman kanta a jihar Kano mai suna Skyline University. Zaman majalisar na jiya ya gudana ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Prof Yemi Osinbajo.
Dayake jawabi ga manema labaran dake dauko rahoto daga fadar shugaban kasa, minister a ma’aikatar Ilimi ta tarayya Farfesa Anthony Awukah ya ce, “A yanzu haka akwai jimlar jami’o’I 163 a kasar nan,daga cikin su masu zaman kansu 73 guda 47 mallakar jihohi yayin da 42 mallakar gwamnatin tarayya.
A hannu guda kuma, ministan ya gargadi jami’o’in gwamnatin tarayya cewa, ba dai-dai ba ne su rinka karbar kudade daga hannun dalibai da sunan kudin makaranta, amma zasu iya karbar kudade domin wasu aikace-aikace da suka shafi lamuran karatu.

en_USEnglish
en_USEnglish