SHUGABAN JAM’IYYAR PDP YA RUBUTA WASIKA GA HUKUMAR EFCC

Shugaban Jam’iyyar PDP Prince Uche Secondus ya rubutawa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu wasikar ankararwa dangane da sanya sunansa a jerin mutanen da ake zargi da satar kudaden gwamnati ba.
Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in labarum shugaban na PDP Mr, Ike Abonyi, Mista Secondus ya ce, “Bai karbi Naira Miliyan 200 ba daga ofishin tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin tsaro Sambo Dasuki ba kamar yadda gwamnatin tarayya ke ikirari.
Wasikar ta tunatar da hukumar EFCC cewa,batun wannan zargi na gaban kotu,  don haka sai Prince Secondus yayi mamakin yadda hukumar ta EFCC ta gaza tunkarar kotun da hujjojin da take dasu, amma maimakon haka ta zabi amfani da kafafen yada labarai.

en_USEnglish
en_USEnglish