A YAU AKAYI JANA’IZAR SHAIK ISIYAKA RABI’U.

Da misalin karfe biyu da talatin da hudu ne na rana aka gudanar da sallar jana’izar shugaban darikar Tijjaniya na Afrika marigayi Sheikh Isyaka Rabi’u a masallacin sa dake unguwar Goron Dutse a yau juma’a.

Babban limamin masallacin kaulaha dake kasar Senegal, Sheikh Aliyu Cisse ne ya gudanar da sallar jana’izar marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rab’iu.

A cikin mutanen da suka halarci sallar jana’izar akwai manya manyan baki daga ciki da wajen kasar nan a ciki akwai gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarakunan gargajiya ciki da wajen jihar nan da kuma shugaban rundunar sojin kasar nan Janar Tukur Yusuf Burutai da dai sauran su.

An dai binne marigayi Shiekh Khalifa Isyaka Rabi’u a cikin masallacin sa dake unguwar Goron Dutse a nan Kano.

en_USEnglish
en_USEnglish