DAKARUN SOJA SUN KASHE YAN BINDIGA GUDA TAKWAS.

Dakarun soja sun kashe wasu yan bindiga guda takwas a yayin wani musayar wuta a yankin karamar hukumar maru ta jihar zamfara, hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Kasarnan  Majo Clement Abiade wadda aka rabawa manema labarai a jiya,”yace dakarun sojan na gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na musamman  a sassan jihar Zamfara wadda ke fuskantar barazanar tsaro.

Sanarwar ta kara da cewa, jami’an sojan sunyi wa yan bindigar kofar rago ne a wani daji dake  garuruwan Dansadau da Koboro da kuma Sangeko dukkanninsu a yankin karamar hukumar  Maru ta jihar Zamfara.

Sanarwar ta ci gaba da cewa,baya ga yan bindiga guda takwas da sojojin suka samu nasarar kashewa a yayin karanbattar, sun kuma raunata wasu da dama.

en_USEnglish
en_USEnglish