GWAMNATIN KASAR SALIYO ZATA FARA BAYAR DA ILMI KYAUTA.

Sabon shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya ce gwamnatin sa za ta fara bada ilimi kyauta ga daukacin daliban makarantun Firamare da na sakandire dake fadin kasar tun daga watan Satumbar bana.

Julius Maada Bio, ya bayyanawa majalisar dokokin kasar dake birnin Freetown cewa, za a rubanya kasafin kudin a bangaren ilimi.

Ya ce za a samar da kudin ne dan rage kashe kudin a wasu bangarorin, sannan kuma zai nemi tallafi daga kasashen ketare.

Rahotanni na nuni da cewaa, kasar Saliyo na daya daga cikin kasashen duniya masu fama da matsanancin talauci, kuma fiye da rabin al’ummar kasar na fama da karancin rashin iya karatu da rubutu.

en_USEnglish
en_USEnglish