KIMANIN YARA DUBU DARI TAKWAS KE FAMA DA KARANCIN ABINCI MAI GINA JIKI.

Majalisar dinkin duniya ta ce, “yara dubu dari hudu ne a yankin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ke fama da matsanancin karancin abinci mai gina jiki.
Sanarwar na kunshe ne a cikin wani rahoto da asusun kula da kananan yara na majalisar wato UNICEF ya fitar, ta ce kananan yaran na matukar bukatar dauki na gaggawa domin ceto rayukan su.
Rahoton ya kuma bukaci a samar da Karin kudaden da za a yi amfani da su wajen kara yawan cibiyoyin samar da abinci mai gina jiki ga kananan yaran dake fama da yunwa.
Yankin na Kasa, wanda a baya ya kasance daya daga cikin wadanda aka fi zaman lafiya a kasar ta Congo ya fada cikin rikici a shekarar 2016, lamarin da ya janyo dubbban al’umma rabasu da muhallin su.
Asusun ya kuma yi kiyasin cewa kusan yara dubu dari 8 ne ke fama da karancin abinci mai gina jiki, kuma matukar ba a tallafa musu da gaggawa ba, akwai yuwar su rasa rayukan su.
Haka zalika UNCEF ya kuma bukaci tallafin kudi dala miliyan 88 domin aikin agaji a yankin na Kasai dake jamhuriyar Deomkradiyar Congo.

en_USEnglish
en_USEnglish