SHUGABA BUHARI YACE YANA SANE DA HALIN DA AL’UMMAR KASAR NAN KE CIKI.

Gwamnan jihar Jiagawa, Abubakar Badaru, ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban da ya ke daura kasar nan a kan gwadaban ta, duba da yadda yake yaki da rashawa da kuma farfado da tattalin arzikin kasar nan, tare da kuma samar da tsaro.
Abubakar Badaru ya bayyana hakan ne a birnin Dutse dake jihar Jigawa a yau dinnan yayin da yake gudanar da jawabin sa, ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya ce irin ayyukan da shugaban kasa ke gudanarwa, ya nuna cewa, ya cirri tuta, duba da yadda al’umma ke amfana.
Ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya aiwatar da sababbin ayuka a jihar ta Jigawa, musamman ma wajan shimfida tituna da samar da ruwan sha a jihar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa al’ummar kasar nan da su kara hakuri duba da yadda ‘yan kasar nan suka tsinci kan su a cikin wani mawuyacin hali.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a safiyar yau dinnan yayin gudanar da jawabin sa ga daukacin al’ummar jihar Jigawa a birnin Dutse, cewa ba zai bari a ci amanar al’ummar kasar nan ba.
Ya ce ‘yan Nijeriya da su kara hakuri sabida yasan halin da al’umma ke ciki a halin yanzu.
Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Jigawa, tun bayan darewa kan karagar mulki, wanda ya bude wasu ayuka da gwamnatin jihar ta aiwatar ciki harda tituna da ruwa da kuma harkokin noma.
Sannan kuma a yau ne Shugaban zai koma birnin tarayyar Abuja, inda zai i bude sabon shelkwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (EFCC) a Jabi.

en_USEnglish
en_USEnglish