TSOHON SHUGABAN MAJALISAR KANO YA TSIGE WASU YAN MAJALISA MASU RIKE DA MUKAMAI.

Da misalin karfe 11 da minti 42 ne, ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, su 24 karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar Kabiru Alhassan Rurum suka isa harabar majalisar, dauke da kwafin sandar majalisar sakamakon dauke waccan da aka yi sannan kuma suka tsige wasu ‘yan majalisu masu rike da mukamai.
Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana cewa sun tsige ‘yan majalisun ne bisa rashin can-cantar su da kuma gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba,kuma tuni suka maye gurbin su da wasu ‘yan majalisun.
Ya ce sun tsige dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Warawa kuma bulaliyar majalisar Labaran Abdul da kuma Bello Bututu mataimakin shugaban masu rinjaye inda suka maye gurbin su da iliyasa Abdul Yar-yasa dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada a matsayin bulaliyar majalisar, sai kuma iliyasu Labaran Durum dan majalisa mai wakiltar Kabo a matsayin mataimakin masu rinjaye.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito mana cewa, kasancewar basu cika su 27 kamar yadda doka ta tanada shi yasa basu tsige shugaban majalisar ba.

en_USEnglish
en_USEnglish