GWAMNAN JIHAR KANO YA SULHUNTA ‘YAN MAJALISAR DOKOKIN KANO DA SUKE RIGIMA DA JUNA.

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya warware rikicin da ya mamaye Majalisar Dokokin Jihar Kano tsakanin Shugaban majalisar, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata da kuma wasu sauran mambobin majalisar.

Wata majiya mai tushe a cikin majalisar jihar ta shaidawa manema labarai cewa, an warware rikicin majalisar ne yayin ganawa ta musamman tsakanin gwamnan jihar Kano da duka tsagi biyun.

Majiyar ta ce, an warware matsalar ne a taron wanda ya gudana a daren jiya, dukansu sun bayyana gamsuwarsu yayin sasantawar da gwamnan yayi masu.

tsagin ‘yan majalisun masu rigima da shugaban majalisar dokokin sun amince da cewa Yusuf Abdullahi Ata ya ci gaba da zaman sa a matsayin shugaban majalisar, yayin da kuma tsohon shugaban majalisar Kabiru Alhassan Rurum zai zama mataimakin sa.

Haka kuma sun amince da Bello Bututu a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.

A safiyar jiya ne dai wasu daga cikin tsagin majalisar masu adawa da shugaban majalisar suka bada sanarwar tsige wasu manyan masu rike da mukaman majalisar a harabar majalisar bayan girke jami’an tsaro da aka yi.

en_USEnglish
en_USEnglish