HUKUMOMIN SAUDIYYA SUNCE A GOBE ALHAMIS NE ZA’A FARA AZUMIN RAMANDANA .

Hukumomin Saudi Arabiya sunce a gobe alhamis ne za’a fara ibadar watan azumin Ramadana na shekarar 1439

Kamfanin dillanacin labarai na Saudiyya ya rawaito mahukuntan kasar na cewa, kasancewar, watan na Ramadana bai bayyana ba a jiya talata, yau laraba ta kasance 30 ga watan sha’aban kuma gobe alhamis zata zama daya ga watan Ramadana.

don haka hukumomin na Saudiyya suka ayyana gobe alhamis a matsayin ranar da daukacin al’ummar musulmi zasu fara ibadar azumin Ramadana.

A hannu guda kuma, majalisar fatawa na kasar masar tace a gobe alhamis din ne al’umar kasar zasu fara azumi

Haka al’amarin yake a kasashen Jordan da Iraqi da kasar hadaddiyar daular larabawa

en_USEnglish
en_USEnglish