KASAR AFRIKA TA KUDU TA JANYE JAKADANTA DAGA KASAR ISRAILA.

Kasar Afirka Ta Kudu ta janye Jakadanta daga kasar Isira’ila jiya Talata, bayan da sojojin Isira’ila su ka kashe mutane 60 daga cikin Falasdinawan da ke zanga-zanga akan bude ofishin Jakadancin Amurka a birnin Kudus da ake takaddama a kai.

Sashin Harkokin Cudanyar Kasa da Kasa da Hadin Kai na kasar ya yi Alawadai da matakin da sojojin Isira’ila suka dauka game da Falasdinawan da ke zanga-zanga a Gaza, cewa, Wadanda abin ya rutsa da su na zanga-zangar lumana ne kan takalar da Amurka ta yi, wajen kaddamar da Ofishin jakadancinta a Birnin Kudus.

A cewar Sashin, ya sa Afirka ta Kudu ta gaggauta janye jakadanta daga birnin Tel Aviv, inda akasarin Ofisoshin Jakadancin kasashe su ke a kasar ta Isira’ila bisa wannan tashin hankalin day a auku.

Masu zanga-zangar, wadanda yawansu na sanye da riguna masu dauke da sakon da ke cewa, “A ‘Yantar da Falasdinu da kuma wanda ke cewa, A tsai da Manufofin Wariya Na Isira’ila, ciki har da wata ‘yar kungiyar mutanen da ke kiran kansu “Yahudawan Afirka ta Kudu” ‘Yan Rajin ‘Yantar da Falasdinawa.

 

en_USEnglish
en_USEnglish